Buhari ya ce zai tabbatar da sahihin zaɓe a 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ƴan Najeriya da sauran ƙasashen duniya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe a 2023, tare da mika mulki cikin kwanciyar hankali.

A jawabin da ya yi a wajen wani taron da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya, shugaba Buhari ya ce za a ƙarfafa hanyoyin da suka dace don tabbatar da cewa an samu sauyin mulki cikin kwanciyar hankali da lumana, kamar yadda sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta bayyana.

Sanarwar ta ce, Buhari ya shaida wa Biden cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan mulkin ɗimokuradiyya a yammacin Afrika da Afrika baki ɗaya, kuma Najeriya za ta ba ƙungiyoyin Ecowas goyon baya wajen magance wannan ƙalubalen da kuma godiya ga goyon baya daga Tarayyar Afrika da Majalisar Ɗinkin Duniya.