Buhari ya aike da sakon dubiya ga Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din da ta gabata ya yiwa Sheikh Mohammed Dahiru Bauchi fatan samun sauki daga rashin lafiya.

Shugaban a sakon da ya aikewa jagoran kungiyar Tijjaniyya ta Darikar Tijjaniyya, wanda Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Farfesa Isa Ibrahim Ali Pantami ya mika a madadinsa, ya ce yana yi wa Sheikh fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya yi addu’ar Allah ya kara wa jagoran addinin Musulunci lafiya domin ya ci gaba da jagorantar mabiyansa da al’ummar kasar nan a kokarin gina al’umma mai adalci da tausayi.


“Addu’ata ta koma gare shi. Allah ya kara masa lafiya da samun lafiya cikin gaggawa,” inji shi.
Sai dai Pantami ya kai rahoto ga shugaban kasar cewa halin da Sheikh din ke ciki yanzu ya yi kyau.
Ya kara da cewa shugaban na addinin musuluncin ya godewa shugaban kasar bisa kulawar da ya nuna masa, tare da addu’ar Allah ya ci gaba da samun nasarar gudanar da mulki a bangaren gina kasa, zaman lafiya da ci gaba.