Buhari Bai San Barazanar ‘Yan Ta’adda Ba Sai da Na Sanar Da Shi – El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce shi ne ya gaya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari game da barazanar ‘yan ta’adda na sace shi….
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce shi ne ya shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari game da barazanar ‘yan ta’adda na sace shi. A wani faifan bidiyo da aka fitar a karshen mako, ‘yan ta’addan da suka sace wasu fasinjojin jirgin kasa a watan Maris, sun yi barazanar sace Buhari da El-Rufai.
Da yake magana a wani shirin gidan rediyo da Wakilinmu ya sanyawa ido a daren ranar Laraba, gwamnan ya kuma ce shi da kansa an gargade shi da ya yi hattara har da iyalansa. Ya ci gaba da bayanin cewa shekaru biyar da suka gabata yana bayar da shawarwarin kai harin bam a sansanonin ‘yan ta’adda a duk inda suke, yana mai cewa ita ce kadai mafita ga matsalar. “Na kuma ji labarin wani faifan bidiyo inda suka yi barazanar sace Buhari da ni kaina. An gargade ni da in yi hattara har da iyalaina ma. Ta yaya za mu kasance a kasar da sojoji da ‘yan sanda da gwamnatin tarayya amma wasu ‘yan ta’adda za su yi barazanar sace shugaban kasa? “Idan a baya wadanda ke cikin gwamnati suna ganin wannan abin wasa ne kuma suna ganin abin yana faruwa ne a Katsina, Zamfara, Kaduna da Neja, yanzu yana gida kuma dole ne mu tashi mu yi maganin wadannan mutane. Wannan ne ya sa na gana da shugaban kasa a ranar Lahadi na gaya masa wadannan matsalolin. Ni ma na ba shi labarin bidiyon domin har zuwa wannan rana bai ma san da shi ba. Sai na ce masa da washegari gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, shi ma ya tabbatar masa da cewa shi ma ya ga bidiyon ne domin ya dauki mataki. “Shugaban kasa ya tabbatar mani da cewa ya gana da hafsoshin tsaro kwanaki 3-4 kafin ganawar tamu kuma ya ba su umarni karara cewa su gudanar da cikakken aikin soji don tunkarar wadannan mutane. Muna fata, da yardar Allah sojoji da ’yan sandan da aka ba wa umurnin za su gaggauta kammala aikin. Ba sai mun jira sai su (‘yan ta’adda) su kai farmaki kafin mu mayar da martani.
“Dole ne su (sojoji) su bi su duk inda za su yi da su. Maganar gaskiya mun damu da matsalar tsaro amma muna fatan gwamnatin tarayya za ta yi abin da ya dace,” inji shi.