Budurwa ta cinna wa saurayinta wuta a Benue
Yi tunanin kana cikin barci tare da budurwarka a kan kafaɗarta, tana sumbatarka tare da yi maka murmushi, kwatsam sai ka farka ka ganka a ƙone, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarka.Wannan ne labarin Elvis Chidinma Omah, wani mai sayar da magani a kemis a Makurdi, babban birnin jihar Benue state,a arewa ta tsakiyar Najeriya.Elvis Chidinma Omah da budurwarsa mai shekara 17 masoya ne na haƙiƙa da suka shafe shekara uku suna soyayya.Kowace rana soyayyarsu na ƙaruwa tare da yin alƙawarin kasancewa da juna har abada, kuma za su yi aure na mutu ka raba.Amma yarinyar ta fara cire rai bayan da ƙawayenta suka ce mata masoyin nata ya kai wa wata budurwar daban kuɗin aure a ƙauyen nasu.Duk da cewa Omah ya yi ƙaryata labarin, matashiyar mai shekara 17 ba ta gamsu da bayanin da ya yi mata ba, kuma burinta shi ne ta kawo ƙarshen soyayyar ta hanyar cinna wa gidansa wuta.
Wutar da ta kashe ƙishirwar soyayya
Omah ya far soyayya da yarinyar ne kusan shekara uku da suka gabata, kuma rahotanni sun ce shi ne ya fara saninta ƴa mace.
Ta shaida wa ƴan sanda cewa ya yi mata alƙawura da dama ciki har da na aurenta kuma har rantsuwa sun yi kan hakan.
Mai magana da yawun ƴan sanda Catherin Anene ta ce da suka tambayi yarinyar sai ta ce musu a da komai yana tafiya sumul tsakaninta da shi, kwatsam daga bisani sai ya sauya.
Ta samu ciki da shi Elvis Chidinma Omah sai kawai ya sauya halaye ya dinga bin wasu ƴan matan yana kai wa gidansa, kuma idan dare ya yi sai ya ce mata ta kwanta a ƙasa shi kuma sai ya haye gado da sabuwar budurwa.
Saboda son da take masa da burin aurensa sai ta shanye komai ta haƙura.
Daga baya sai ya ce mata ta zubar da cikin, ta sake ɗaukar na biyu ma ya ce ta zubar, sannan ya sake sa wa ta zubar da na ukun ma – daga nan ne ta ji haushi har suka ɓata da shi.
Matashiyar mai shekara 17 sai ta zana jarrabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB don fara sabuwar rayuwa ta kuma shiga jami’ar, inda a lokacin ne Omah ya koma ya sake lallashinta cewa su koma kamar da.
Ta ƙi amincewa, amma bayan roƙo da rarrashi sai ta masa alƙarin cewa za ta je ta gan shi ranar Lahadi, a hanyarta ta zuwa ne ta sayi fetur na naira 870 da kuma ashana.
SUMBAR YAUDARA
Elvis Chidinma Omah a lokacin bai daɗe da dawowa daga ƙauyensa da yake Nsuka a jihar Enugu ba.
Don haka ziyarar da masoyiyar tasa ta kai masa gidansa da ke titin Zaki Biam a yankin Wadata da ke Makurdiba ƙaramin farin ciki ya sa shi ba.
Ta yi musu girki mai daɗi suka ci suka yi hani’an, kuma ba ta nuna wata alama ta ƙullatarsa ba.
Yarinyar ta shaida wa manema labarai cewa bayan da suka yi abin da suka yi har Omah ya samu barci, can wajen ƙarfe 2 na asubahin Litinin wato 11 ga watan Janairun 2021, sai ta ɗauko wannan fetur ɗin ta watsa a duk ɗakin, ta cinna wuta ta gudu wani coci.
Omah ya tashi a gigice cikin ihun da ya tashi wasu maƙwabtansa da suka yi maza suka kai shi asibiti. Kafin sannan ƙunar ta yi yawa – suka yi maza suka garzaya da shi babban asibitin Federal Medical Centre amma zuwa washegari ranar Talata ya ce ga garinku, kamar yadda rundunar ƴan sanda Benue ta ce.
Ƴan dandan waɗanda suka ce a yanzu yarinyar na hannunsu a tsare, sun ce za su kai ta kotu bayan sun kammala bincikensu.
A makonnin da suka gabata dai yawan masoyan da suke ƙona kansu na ƙaruwa sosai a Binuwai.
Wani mai shekara 40 Nicodemus Nomwange ma ya cinna wa kansa da masoyiyarsa Shiminenge Pam wuta, kuma a daidai wannan lokacin ma wata matar ta ƙona saurayinta a garin Gboko.