Bello Turji: Yadda mutane suka yi rayuwa a hannun dan bindigar
A makon nan ne ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan da aka fi sani da Bello Turji ya saki wasu gomman mutane da suka daɗe suna tsare a hannunsa.
Bello Turji dai na daga cikin manyan ƴan fashin dajin da ke Najeriya da ake nema ruwa a jallo sakamakon irin hare-haren da yake kai wa shi da yaransa.
Wani daga cikin sama da mutum 50 da Bello Turjin ya saka mai suna Ahmad Abdulrazak, wanda yaran Bello Turji suka sace a hanyar Kaura Namoda zuwa Sabon Birni ya ce sun sha baƙar wuya a hannun Turji.
A wata hira da ya yi da tashar Mai Biredi TV ta Youtube, ya bayyana cewa ya shafe kwana 32 a hannun masu garkuwan, amma duk tsawon waɗannan kwanakin bai samu ganin uban gayyar ba wato Bello Turji.
Ahmad ya bayyana cewa ƴan bindigan sun faɗa musu abubuwa da dama, inda daga ciki suke yawan ba su labarin cewa a rayuwarsu babu abin da suke tsoro kamar jirgin soji.
Ƴan bindigar sun shaida masa cewa idan jami’in tsaro ya je wurinsu a ƙasa lallai za su illata shi, ya kuma bayyana cewa har nema suke sojoji su zo wajen su a ƙasa domin su illata su.
“Da sun ga jirgin sojoji za su ɗauremu da kaca su ƙara tsuke mu su tsere su je wajen dutsi su ɓoye,” in ji Ahmad Abdulrazak.
Ya ƙara da cewa sojoji ba sa shiga cikin dajin a ƙafarsu , jirgi ne ke shiga.
Ya bayyana cewa sun ga jirgin soji ya shiga daji sau da dama har ya taɓa jefa musu bam ɗin da ya kusan illata su sakamakon wutar da ta tashi bayan jefa bam ɗin da jirgi ya yi.
Ahmad ya tabatar da cewa bam ɗin da jirgin yaƙin soji ya jefa a cikin daji har sai da ya ƙona makarantar Turji da kuma kayan abincinsa.
Ya bayyana cewa jirgin bai illata ko mutum ɗaya ba cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, amma kuma ya illata wasu daga cikin yaran Turji da makamansu inda har mutum guda ya rasu.
Ahmad ɗin ya bayyana cewa ya ji ɗaya daga cikin yaran Turjin na cewa mai gidansu ya bayar da kuɗi naira miliyan biyu a kai ɗaya daga cikin yaransa da jirgi ya illata zuwa asibiti.
Yadda Turji ya saki sama da mutum 50
Ahmad Abdulrazak ya bayyana cewa suna zaune a cikin daji sai wani ya zo da kayan sojoji ya tambayi waɗanda ke tsaren su ƴan wane gari ne? Sai suka ce su mutanen Kauran Namoda ne, sai ya tambaye su suna so su tafi gida sai suka ce suna so.
A cewarsa, nan take ya sa aka kwance su ya ce musu duk wanda ya gudu za a kashe shi.
Ya bayyana cewa daga nan ne aka haɗa su da yara ƴan shekara kimanin shekara 13 waɗanda aka ba su umarnin su raka su su fitar da su bakin wasu gezoji.
‘Bakin gulbi Bello Turji ya ajiye su a kusa da ƙauyen Mabera’
JARIDAR BBC ta wallafa cewa ta ji ta bakin wani wanda ya ga wasu daga cikin wadanda aka sako daga dajin.
“Da misalin ƙarfe biyar na maraice zuwa shida, shi Bello Turji ya sako waɗannan mutane, kuma aka je aka zo da su zuwa Area Command na rundunar ‘yan sanda da ke nan cikin garin Shinkafi.”
Ya ce ba da jimawa ba kuma aka wuce da su zuwa Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Ya kara da cewa “wasu cikin ‘yan uwan wadanda aka sakon sun gana da su har ana ta murna.”
Da aka tambayi wannan shaidan ko a me aka kwaso wadanda aka sakin, sai ya ce: “An kawo su ne a motoci. Bakin gulbi Bello Turji ya ajiye su a kusa da wani ƙauye da ake ce ma Mabera da bai wuce kilomita uku ko hudu ba daga garin Shinkafi.”
An kuma tambaye shi ko mutum nawa aka sako, inda ya ce, “Gaskiya duka ya sako, amma ba zan iya tantance yawansu ba saboda suna da yawa sosai.”
Ya ce akwai wadanda suka ce wadanda aka sakon sun kai mutum dari, amma shi dai bai iya ƙirga su ba.
Wannan ganau ɗin ya bayyana cewa Bello Turji ya sako dukkan wadanda yake garkuwa da su ne saboda yana neman hanyar sasantawa da hukuma ne.
“Yana neman ya ga ya daidaita lamurra ne domin a zauna lafiya. Dukkansu ya sako.”
Ya ce cikin wadanda aka sako, akwai maza da mata har ma da ƙananan yara.
“Wasu cikinsu ma suna ɗauke da raunuka, domin lokacin da aka tare su bisa hanya, barayin dajin sun bude musu wuta kuma wasu an harbe su sai dai harbin ba mai matsala ba ne, kuma a haka suka tafi da su daji suka tsare su.”
Ya kuma kara bayyana halin da ya gansu: “Idan ka dube su za ka ga kamar an haƙo su daga cikin kasa ne saboda halin da suke ciki na rashin wanka da rashin wanki, kuma ga ƙura suna zauna a fili cikin daji.”