Batun Karba-Karba Ba Abin Fada Ba Ne – Lalong

A Najeriya, yayin da jam`iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar da babban taronta, wani kalubalen da take fuskanta shi ne yadda za ta tunkari batun karba-karba.

Har yanzu dai jam`iyyar ba ta fadi yankin da za ta bai wa shugabancin kasar ba da kuma shiyyar da za ta fitar da shugaban jam`iyyar ba.

A karshen wannan watan na Fabrairu ne ake sa ran za a yi babban taron jam`iyyar inda za ta zabi shugabanninta na kasa.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC na arewacin kasar, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam`iyyar wadanda ke kokarin nema mata mafita.

A wata hira ta musamman da Muryar Amurka Gwamna Lalong ya shaida mana yadda yake kallon lamarin.

Ya ce lokacin da ‘yan kudu suka fito suka ce lalle ne shugaban kasa ya fito Daga kuda, su sun ce siyasa ba abin gori bane amma sun samu fahimtar juna akan hakan.

Ya ce dole ne a taron Jam’iyyun a samu sabani, kuma su idanun su na kan shugaban kasa Buhari amma tun da yanzu zai tafi, kowa ya neman abin duba.