Barazana Ga Rayuwar Mata Da Yara
Cin Zarafi Tsakanin Ma’aurata Na Barazana Ga Rayuwar Mata Da Yara
Fiye da shekaru shida bayan majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudirin dokar dake bada kariya ga iyalai musamman mata da yara daga dukkanin nau’in cutarwa, har yanzu masu ruwa da tsaki na fafutukar ganin gwamnatin jihohin sun kafa tare da zartar da samfurin wannan doka a jihohin su. WASHINGTON DC —
Yaki da aikatau, fyade da cin zarfi tsakanin ma’aurata da sauran nau’ika na tauye ‘yanci da barazana ga makomar rayuwa mata da yara na daga cikin al’amuran da dokar ke kokarin kawarwa a cikin al’uma.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da taron masu ruwa da tsaki na kwanaki uku a kan yadda za’a aiwatar da wannan doka a jihar Yobe ke gudana a Kano.
Malam Musatafa Wakil shine sakataren kwamitin JRT dake aikin gudanar da garanbawul a sashin shari’a na jihar Yobe, ya ce sun sun taba alli da dukkanin masu ruwa da tsaki gabanin samar da daftarin dokar.
Yanzu haka dai majalisar dokokin jihar ta Yobe ta amince da kudirin dokar kuma ana dakon gwamna Mai Mala Buni ya rattaba, amma kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa reshen jihar ta fara aikin fadakar da mutanen jihar game da kunshin dokar, inji Sakatariyar kudin kungiyar,
Tun a cikin watan Yunin bana ne, gwamnan Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya rattaba hannu akan wannan doka bayan gyaregyaren da majalisar dokokin jihar tayi.