Barau ya ba da tallafin karatu ga ƙarin ɗalibai 870

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, a ranar Talata, ya fara kashi na biyu na shirin bayar da tallafin karatu tare da dalibai 870 na Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano (YUMSUK).

Daliban da aka zabo daga mazabar Kano ta Arewa, inda dan majalisar ke wakilta, an bai wa kowannensu Naira 20,000.

Da yake jawabi yayin rabon kudaden a harabar jami’ar, shugaban ma’aikatan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce Barau ne ya kirkiro shirin domin tallafa wa daliban mazabarsa.

Sanarwa daga ofishin yada labarai na Sanata Barau ta ce an fara shirin bayar da tallafin ne a watan Agusta da dalibai 628 na Jami’ar Bayero Kano (BUK).

“Kowane daya daga cikin daliban zai samu kyautar Naira 20,000 daga hannun Sanata Barau kuma duk dalibin Kano ta Arewa da ke karatu a Najeriya zai ci gajiyar wannan shirin. Mun fara ne a watan Agusta tare da daliban BUK, kuma yau muna YUMSUK kashi na biyu,” inji shi.

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan damar su yi karatun ta nutsu domin su yi fice a harkar ilimi.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Ummussalam Haruna Yusuf, daliba mai matakin 300, ta godewa mataimakiyar shugaban majalisar dattawa bisa wannan karimcin.

“Babban kalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne harkokin sufuri da abincin da za mu ci yayin da muke makaranta. Wannan karimcin da Sanatanmu ya yi zai taimaka mana a kan haka,” inji ta.