Ban Matsu dole sena zama Shugaban kasar Nigeria a shekarar 2023 ba___ Inji Dr Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dan Takarar Shugaban kasar Nigeria karkashin Jam iyar NNPP Alhaji Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce shi Takarar Shugaban kasar Nigeria da yake yi ba ta ko a mutu ko ayi rai bace. Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce shi ba wai ya matsa dole sai ya zama Shugaban kasar Nigeria a zaben 2023 Mai zuwa ba.

Kwankwaso ya ce shi da makaman tansa sun shiga Jam iyar NNPP ne domin ceto Yan’ Nigeria.

Yace kowanne cikakken Dan kishin kasa dole ya damu da matsalar tsaro, Tattalin Arziki kuma dole ya na bukatar samun Shugaba na gari.

Kwankwaso ya ce don haka shi bawai yafita daga Jam iyar PDP ya shiga Jam’iyar NNPP don dole sai ya zama Shugaban kasar Nigeria ba.