Badakalar N187bn: EFCC ta kama dan kwangilar ma’aikatar jin kai, ta binciki ministocin Buhari hudu
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta kama wani dan kwangila mai suna James Okwete, kan binciken da ake yi kan N37bn da ake zargin ma’aikatar kula da jin kai, da yaki da bala’o’i da ci gaban jama’a a karkashin tsohuwar Minista, Sadiya Umar-Farouk.
Wani babban jami’in hukumar ta EFCC, wanda ya shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi, ya ce dan kwangilar ya yi wasu bayanai masu amfani game da tsohuwar minsta da kuma tsoffin daraktocin ma’aikatar.
Wannan ci gaban ya zo daidai da binciken wasu ministoci uku, wadanda suka yi aiki a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan zargin almundahana da aka kiyasta ya kai N150bn.
“Ba Sadiya Umar-Farouk kadai muke bincike ba. Ana kuma binciken wasu tsoffin ministoci uku. Ana zarginsu da hannu a badakalar N150bn,’’ wata majiya mai tushe a cikin EFCC ta bayyana wa wakilinmu a ranar Lahadi.
Majiyoyi sun ce Umar-Farouk da wasu tsoffin manyan daraktocin ma’aikatar za su iya kama hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa biyo bayan bayanan almubazzaranci da kudaden da dan kwangilar ya yi wa masu binciken har yanzu.
An kasa samun tsohon ministan domin jin ta bakinsa ranar Lahadi. Haka kuma, lokacin da wakilinmu ya tuntubi tsohuwar mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Nneka Ikem, ba ta dauki wayarta ba, haka kuma ba ta amsa sakon SMS da aka aika mata ba.
Bincike ya nuna cewa an fitar da N37.1bn daga asusun gwamnatin tarayya kuma an aika zuwa asusun banki daban-daban 38 da ke cikin wasu bankunan kasuwanci na gado biyar na Okwete ko kuma ke da alaka da su.
A cewar jami’an EFCC, an kama dan kwangilar ne kwanaki hudu da suka gabata.
Wata majiya ta ce, “Hukumar ta kama dan kwangilar, Mista Okwete, wanda aka yi amfani da shi wajen karkatar da kudaden. A yanzu haka yana tsare a hannunmu, kuma yana yi wa masu bincike karin bayanai da suka tuhumi tsohuwar Ministar, Sadiya da wasu shugabannin ma’aikatar, kuma za a iya shigo da su nan ba da jimawa ba.”