“Babu wata tantama idan aka samu shugaban ƙasa daga cikin ministocin nan za a ga cikakkiyar ƙwarewa da kuma tsabar aiki ga al’umma,” – BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ban-kwana da ministocinsa da suka ajiye aiki don yin takara a babban zaɓe mai zuwa na 2023. 

Yayin jawabinsa, Buhari ya ce ya yi imani da yawa daga cikin ministocin na da ƙwarewar da za su iya gadar sa. 

“Babu wata tantama idan aka samu shugaban ƙasa daga cikin ministocin nan za a ga cikakkiyar ƙwarewa da kuma tsabar aiki ga al’umma,” in ji shi. “Wannan na ɗaya daga cikin tarihin da za mu bar wa ‘yan Najeriya.” 

A ranar Laraba ne Buhari ya umarci dukkan ministoci da shugabannin hukumomi da ma’aikatu masu son tsayawa takara a muƙamai daban-daban da su ajiye ayyukansu nan da ranar Litinin mai zuwa. 

Daga cikin ministocin da suka yi ban-kwana da shugaban a yau har da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda rahotanni ke cewa zai yi takarar gwamna a jiharsa ta Kebbi. 

Sauaran su ne: Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, Ministan Ƙwadago Chris Ngige, Ƙaramin Ministan Man Fetur Timpre Sylva, Ministan Neja Delta Godswill Akpabio, Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen. 

Sai kuma: Ƙaramin Ministan Ma’adanai Uche Ogah, Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, Ƙaramin Ministan Neja Delta Tayo Alasoadura.