Ba likitan da ke bin mu bashi – Gwamnatin Najeriya
Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige, ya ce babu wani likita a ƙasar da yanzu haka yake bin gwamnatin tarayya bashin ko anini.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kwamitin shugaban ƙasar kan ƙayyade albashi, jim kadan bayan ganawa da gayammar kungiyoyin ma’aikatan lafiya na Najeriya a Abuja.
Ya ce yin wannan bayani ya zama dole, don kore iƙirarin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta kasar NARD da yanzu haka ke yajin aiki ta yi.
”Sun je suna gaya wa yan Najeriya cewa mun rike musu albashi, sannan ba ma ɗaukar harkar lafiya da muhimmanci, wannan ba gaskiya bane ko kadan” inji ministan.
Ya ce ”Sun ɓoye wa jama’a cewa ƴan uwansu da suke ikirarin an riƙewa albashin an ɗauke su aiki ne ta haramtacciyar hanya, don haka gwamnati bata ma san da su ba”.