Anga watan AZUMIN Ramadhan a Saudiyya
Shafin Facebook na Masallatan Harami biyu masu daraja ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa, tare da nuna Sallar Magariba kai-tsaye daga masallacin.
Ganin watan ya sa gobe Juma’a za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1441, wanda ya zo daidai da 24 ga watan Afrilun 2020.Tsallake Facebook wallafa daga Haramain Sharifain
Karshen Facebook wallafa daga Haramain Sharifain
Hukumar Masallatan ta sanar da cewa a ranar Alhamis da daddare ne za a fara gabatar da Sallar Asham, inda Sheikh Shuraim da Sheikh Sudais za su jagorance ta a Masallacin Harami na Makkah, yayin da Sheikh Qasim da Sheikh Budayr za su jagoranci sallar a Masallacin Maznon Allah SAW na Madina.
Azumi a cikin kulle
Azumin bana dai zai kasance daban da yadda aka saba yin sa sakamakon annobar cutar korona da ta sa aka sanya dokar takaita zirga-zirga a kasashe da dama na duniya don hana yaduwarta.
Dama tuni kasar Saudiyya ta sanya matakan kulle tare da rufe duka masallatan kasar, in ban da haramin Maka da Madina, inda a can din kuma aka takaita mutanen da za su dinga halartar sallar.
Haka Kuma a sanarwar ta ranar Alhamis kasar ta jaddada cewa dokokin za su ci gaba da aiki.
Matakan sun hada da:
- Masallatan Biyu za su ci gaba da kasancewa a kulle ga jama’a, ma’aikatan hukumar masallatan ne kawai za a dinga bari suna yi sallolin farilla biyar da kuma asham.
- An rage yawan raka’o’in Sallar Asham daga 20 zuwa 10
- An dakatar da bayar da abincin buda baki a cikin masallatan
- Dakatar da Umara da aka yi zai ci gaba kamar yadda aka hana tun farkon barkewar annobar a kasae
- An soke yin Ittikafi