Ana so a dinga bai wa ƴan mata ƴan makaranta maganin hana ɗaukar ciki

Ƙungiyoyin masu fafutuka suna so a bai wa ƴan mata ƴan makaranta damar samun magungunan hana ɗaukar ciki a Zimbabwe ba tare da sa idon iyaye ba.

Florence Mutake, daga ƙungiyar Shamiri Yemwanasiana, ta shaida wa shirin BBC Newsday cewa mataimakin shugaban ƙasar ya yi watsi da buƙatar, wacce wasu ƴan majalisar dokoki suka gabatar, kan dalilin “aladu da tarbiyya”.

Amma ta ce batu ne da yake buƙatar a fayyace shi saboda fiye da ƴan mata 5,000 ne suka yi ciki ba tare da aure ba a yayin annobar cutar korona – kuma 2,000 daga cikinsu ƴan ƙasa da shekara 16 ne.

An rufe makarantu tsawon watanni saboda kare yaɗuwar cutar.

Ms Mutake ta ce “Ƴan mata na saduwa da maza abin da ke sa suna samun ciki,

“Muna ganin yadda ƴan mata da dama ke zaune a gida babu abin yi.”

A Zimbabwe an bai wa ƴan mata damar su yi aure a shekara 18, yayin da budurwa ke da damar sanin ɗa namiji a shekara 16.

Wasu rahotannin ma sun ce yara kan fara kwanciya da maza tun suna ƴan shekara 10.

Gwamnatin Zimbabwe ta ce kusan ƴan mata 5,000 ne suka yi ciki daga tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu.

Sannan kusan 1,800 ne suka yi aurenn wuri a daidai waɗannan watannin biyu.

Wani rahoton gwamnati ya ce, mafi yawan yaran suna rayuwa ne a unguwannin marasa galihu da ke wajen Harare, babban birnin ƙasar.

Ƴan mata da dama a Zimbabwe na barin makaranta sakamakon yin ciki, lamarin da ka iya jefa su cikin talauci.