Ana kokarin gano wadanda suka yi wa yarinya fyade ‘ta dubura’ suka kashe ta a Kaduna

Ana ci gaba da juyayin rasuwar wata yarinya ‘yar shekara shida, bayan wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka yi mata fyade, a garin Maraban Jos na jihar Kaduna a arewacin Najeriya. 

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, kuma tuni aka yi jana’izar yarinyar. Yanzu haka dai ‘yan sanda suna gudanar da bincike kan lamarin.

A yayin hirarta da BBC Hausa, mahaifiyar yarinyar cikin gunjin kuka da sallallami ta ce idan ta tuna wannan lamarin bakin ciki na damunta matuka a ranta.

Takaici da kaduwa ba su bar mahaifiyar yarinyar ta yi magana mai tsawo kan aukuwar lamarin ba.

Sai dai shugabar kungiyar Ar-Rida da ke taimaka wa mata da yara da gajiyayyu a Najeriya, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim ce ta bayyana yadda lamarin ya faru.

“Abin ya faru ne yayin da yarinyar ke wasa da yara a zaure, da magariba ta yi sai yara suka watse kowa ya shiga dakin mahaifiyarsa, to a lokacin ne uwar ta fahimci yarinyar ba ta gida.

“A lokacin ne aka bazama nemanta amma har bayan isha’i ba a ganta. An tura wasu zuwa wata unguwar neman yarinyar amma ba a ganta ba, sai a hanyarsu ta komawa gida sai suka ga gawarta an jefar a kan hanya,” a cewar Hajiya Rabi.

Sai dai cikin rashin sa’a ba a ga mutanen da suka jefar da gawar tata ba, amma “an same ta jina-jina kuma an tabbatar mana fyade aka yi mata ta duburarta,” a cewar mai rajin kare hakkin mata da yaran.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa ta fara bincike ka’in da na’in don gano wadanda suka aikata wannan mummunan abu.

Karo na uku kenan ana samun aukuwar irin wannan fyade da ke kai wa ga kisa a kasa da shekara guda, a jihar da aka yi dokar yin dandaka ga duk wani namiji da aka samu da aikata laifin fyade.

Tuni kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara suka tashi tsaye wajen ganin ana zakulo masu aikata wadannan laifuka ana hukunta su. 

Hajiya Rabi ta ce an samu raguwar matsalar fyaden tun bayan da Gwamna Nasir El-Rufa’i ya sha alwashin aiwatar da hukuncin dandaka ga masu yi, “amma a gaskiya abin ya dawo a kwanakin baya-bayan nan.

“Irin wannan fyade mai kama da juna an yi sau biyu kenan, wanda ake yi wa yara kanana a kuma kashe su a jefar da gawar, don haka abin da tashin hankalin.”

Shugabar ta Ar-Rida ta ce a ganinta karuwar fyade na baya-bayan nan na da nasaba da rashin gano masu laifin da kuma zartar da hukuncin da aka sha alwashin dauka a kansu.

Ta kara da cewa: “Su ma iyayen yara dole su sake sa ido kan shiga da fitar ‘ya’yansu a kowane lokaci, haka ma muna sake kira ga gwamnati da ta daure ta ci gaba da tabbatar da hukunci musamman ga wadanda dama suke hannunta a tsare.”