Ana jan ƙafa wajen gano ƴaƴanmu da aka sace a Kano – Iyaye

Ana jan ƙafa wajen gano ƴaƴanmu da aka sace a Kano – Iyaye

Manyan mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar PDP sun yi murabus

Bakwai daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP sun yi murabus domin nuna adawarsu da abin da suke kira rashin tsarin shugabancin nagari.

Sai dai sun alkawarta ci gaba da yiwa jam’iyyar biyayya, amma sun ce ba za su ci gaba da shugabanci a kwamitin gudanawar na kasa ba.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa mutanen da suka yi murabus sun hada da mataimakin sakataren kudi da mataimaki kan harkokin shari’a da akawu mai bincike kan harkokin jam’iyya, da mataimakin sakataren yaɗa labarai, da shugabar mata da mataimakin sakataren shirye-shirye.

Mambobin sun zargi cewa akwai rashin tsari na shugabanci da kumbiya-kumbiya a harkokin shugabancin jam’iyyar.

Ukraine na bincike kan kisan ɗan gwagwarmayar Belarus

Ƴan sanda a Ukraine sun kaddamar da wani bincike bayan gano gawar wani dan gwagwarmayar yan adawar Belarus rataye a wani wajen shakatawa da ke Kyiv. 

An ba da rahoton batan Vitaly Shishov a jiya Litinin. 

Wakilin BBC ya ce abokan Shishov sun ce raunukan da aka gani a fuskarsa na nuna cewa ya sha duka. 

Kungiyar da yake yi wa aiki ta ƴan gudun hijra ta ɗora alhakin kisan kan wasu jami’ai da aka turo daga Belarus. 

Ƴar adawar Belarus da ke gudun hijra a birnin London Svetlana Tikhanoskaya ta ce za ta jira sakamakon binciken ba amma a bayyane take karara cewa Shugaba Alexander Lukashenko na zafafa kai hare-hare kan ƴan adawa. 

Ta bayyana hakan a matsayin rauni inda ta ce ya ragewa masu fafutuka su kawo karshen mulkinsa.

Gwamnati ta yi barazanar korar ma’aikatan da ke kwarmata bayananta a sociyal midiya

Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yada wasu ma’aikatan ke wallafa takardun sirri da bayananta a shafukan sada zumunta.

Ta yi gargadin korar ma’aikatan da aka samu da wannan laifi.

Wannan gargadi na kunshe cikin wata sanarwar da shugabar ma’aikatan gwamnati, Dr Folasade Yemi-Esan, ta fitar kamar yada jaridar The Punchtawallafa.

Wannan shi ne karo na biyu da ma’aikatar ke fitar da wannan gargadi kan bankada irin waɗanan takardu, ko a watan Mayun 2020 sai da aka yi wa ma’aikatar irin wannan jankunne.

Canada ta ci tarar Amurkawa 2 da shaidar korona ta bogi

Canada ta ci tarar matafiya biyu daga Amurka, da jami’ai suka ce sun shigo kasar da shaidar yin rigakafin cutar korona na bogi.

An ci tarar kowannen su dala 16,000, bayan masu bincike a filin jirgin sama na Toronto, sun gane shaidar gwajin cutar da na rigakafi ba na gaskiya ba ne.

Wanna na zuwa ne daidai lokacin da Canada ke kokarin sassauta dokokin korona ga matafiyan da suka shigo kasar daga Amurka.

as fined two travellers arriving from the US who, officials say, forged Covid-19 testing and vaccination documents.

Kasashen duniya dai na kokarin sassauta dokokin yaki da cutar korona, a daidai lokacin da wasu ke ganin barkewar cutar a zagaye na uku.

‘Ƙofa a buɗe take don tattaunawa kan yajin aikin likitoci a Najeriya’

Shugaban kungiyar likitocin masu koyon aiki a Najeriya, Dakta Temitope Hussein, ya ce ƙofa a bude take domin tattaunawa kan yajin aikin da suke yin a kasa baki daya.

A tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, Dakta Hussein ya ce za su amince su zauna teburin sulhu da gwamnati, kan batutuwan da suka janyo tafiya yajin aikin da suka hada daalbashi da walwalar jami’ansu da sauran batutuwa masu muhimmanci.

Ya ƙara da roƙon ‘yan Najeriya, su yi hakuri da matakin da kungiyar ta dauka na tafiya yajin aikin.

Wakilin NAN ya shiga asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan a jiya Litinin, inda ya bada bayanin cewa yajin aikin ya shafi harkokin asibitin na yau da kullum.

Ana zargin hukumomin Lebanon da jawo fashewar da ta hallaka mutum 200

Masu rajin kare hakkin bil adama sun zargi mahukuntan Lebanon da sakaci da aikata laifi dangane da mummunan fashewar da ta afku a Beirut cikin shekarar da ta gabata. 

Sama da mutum dari biyu ne suka mutu sanadin fashewar. 

Wani bincike da kungiyar Human Rights Watch ta gudanar ya gano shaida mai karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnati na da masaniya kan illar da ke tattare da sinadarin ammonium nitrate din da adana a tashar jirgin ruwan.

Amma cikin dabara suka amince da jefa rayuwar jama’a cikin hadari. 

Wani bincike na gwamnati kan fashewar ya tsaya cak kuma kusan shekara daya ke nan da faruwar

An fara yi wa ‘yan Tanzania rigakafin cutar korona

An fara yi wa ‘yan Tanzania allurar rigakafin cutar korona, ‘yan kasar sun fara layi a cibiyoyi 550 da aka ware domin gudanar da aikin.

Kasar da ke fuskantar barkewar cutar zagaye kashi na uku, ta karbi tallafin rigakafi miliyan daya samfurin Johnson & Johnson, da Amurka ta bada tallafi karkashin shirin Covax.

Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda aka fara yi wa allurar a makon da ya wuce, ta ce tuni gwamnati ta bada odar karin rigakafin ta hanyar kungiyar Tarayyar Afurka, a wani mataki na ganin ta yi wa kashi 60 cikin 100 na ‘yan kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kawunan ‘yan kasar ya rabu, inda wasu ke nuna damuwa kan ingancin allurar rigakafin.

Shugaba Samia, ta sauya matsayar kasar kan cutar korona, bayan mutuwar wanda ta gada marigayi John Mogafuli, da bai amince da sanya dokar kullen yaki da cutar ba, inda ya ke karfafawa ‘yan kasar yin addua.

Tanzania ce kasa ta karshe a nahiyar Afurka da ta karbi tallafin allurar rigakafin cutar korona.

Ƴan fansho sun yi wa Shugaba Buhari wasiƙa

A Najeriya ‘yan Fansho a kasar ne suka rubutawa Shugaba Muhammadu Buhari wasika, karkashin lemar kungiyarsu.

Wasikar dai ta godiya ce da yabawa ga shugaban kan biyan wasu daga cikin basussukan da suke bin gwamnati.

Wasikar wadda shugaban kungiyar Elder Actor Zal, da sakatare suka rattaba wa hannu, sun bayyana Shugaba Buhari a matsayin shugaban da ke jin koken talakawansa, kuma hakan ya nuna kokarin da gwamnati ke yi na ganin ‘yan fanshon su ma sun dara.

Wasikar ta ce: ”A madadin shugabannin wannan kungiya da mabobinta baki daya muna mika sakon godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan ba da umarnin biyanmu hakkokin mu na shekaru biyu, duk da halin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

“An ba da umarnin biyanmu na watanni 12, sai kuma wasu watanni 6 a watan Yuni, da kuma karin wasu watanni 6 da muke sa ran karba a kowanne lokaci.”

Wasikar ta kara da cewa su na fatan nan ba da jimawa ba za su karbi ragowar kudin watanni 6 ba tare da bata lokaci ko samun wata matsala. 

“A karshe wasi kar ta karkare da cewa, “Ba mu da kalmar da za mu gode maka da ita.”

Ana jan ƙafa wajen gano ƴaƴanmu da aka sace a Kano – Iyaye

Ƙungiyar iyayen yaran da aka sace a Kano ta zargi kwamitin da gwamnati ta ɗora wa alhakin gano sauran yaran da aka sace a jihar daga shekarar 2010 zuwa 2019 da jan ƙafa wajen fitar da sakamakon gwajin ƙwayar hallitta da aka yi wa yaran don tantancewa. 

Koken ƙungiyar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata wata kotu da ke jihar Kanon ta yankewa Mista Paul da ake zargi da sace yaran jihar yana safarar su zuwa jihohin kudancin Najeriya, hukuncin ɗaurin sama da shekara 100 a gidan kaso.

Sakataren kungiyar iyayen da aka sace wa ƴaƴa, Shu’aibu Ibrahim Tajiri, ya shaidawa BBC cewa tsawon lokacin da aka ɗiba wajen samar da sakamakon gwajin kwayar hallittar yara 10 da aka gano a jihar Anambra, ya nuna cewar kwamitin ba da gaske yake aikinsa ba. 

Tajiri ya ce kimanin wata shida kenan da daukar ƙwayoyin hallatar yaran da aka gano a jihar ta Anambra, amma sun gaji da yau da gobe da yan kwamitin ke yi musu, inda suka ce da rabon kwamitin ya zauna an fi wata uku. 

To sai dai a cewar kwamitin gano inda yaran da aka sacen suke, ya ce suna aiwatar da shawarwarin da suka bai wa gwamantin jihar kusan guda 40, ya ce suna aiki tuƙuru kan batun dawo da yaran kuma suna da gwajin kusan yara 6 daga cikin wadanda aka dauki kwayoyin hallartar tasu.

Sai dai kwamitin ya ce suna ci gaba da neman wata mata mai suna Amina Kagara wadda ta tsere tun bayan da aka bayar da ita belinta.

A makon da ya gabata ne dai wata babban kotun a Kano ta yanke wa Paul Owne, jagoran wadan da ake zargi da sace yara a Kano tare da sayar da su jihohin kudu hukuncin daurin shekaru 104 a gidan gyaran hali, bisa zargin aikata lafuka 38. 

Haka zalika a ranar 31 ga watan Disambar bara ne dai iyayen wasu yara fiye da 100 da suka nemi ‘ƴa ‘ƴansu sama ko ƙasa a jihar Kano s ka gudanar da wata zanga-zanga tare da nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin jihar ke jan kafa wajen ceto musu ‘ya’yan nasu.

Daga bisani a farkon shekarar da muke ciki ta 2021 gwamanti Kano ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Mallam Muhammad Garba tace ta gano karin wasu yara 10 a jihar Anambra, kuma ta aike da jakadu dan tantance yaran na Kano ne.

Daga bisani, aka ce sai an yi gwajin kwayar hallitta, saboda samun wasu dake ikirarin wasu daga cikin yaran na Anambra ‘ya’yansu ne da suka bata.