An yankewa ‘Yan fashi shekaru 2 a Nijar
Wata kotun majistare da ke Minna a jihar Neja ta yanke wa wasu barayi Umar Magaji da Abdullahi Mohammed hukuncin daurin shekaru biyu kowanne a gidan yari. Tun da farko, mai gabatar da kara, Inspector…
Wata kotun majistare da ke Minna a jihar Neja ta yanke wa wasu barayin Umar Magaji da Abdullahi Mohammed hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Bello Mohammed, ya shaida wa kotun cewa a cikin watan Satumba, 2022, wani Muhammadu Sani da wasu biyar sun kai wa ‘yan sanda rahoton cewa barayi sun kai farmaki kauyensu na Fulani da ke karamar hukumar Paikoro inda suka sace shanu 12 da tsabar kudi N3.3m.
Ya ce jami’an ‘yan sanda sun kai farmaki inda suka kama Umar Magaji da Abdullahi Mohammed na Minna da kauyen Mayaki kuma sun amsa laifin da suka aikata a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike.
Alkalin kotun, Adamu Abubakar, ya yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu kowanne amma ya ba su zabin biyan N140,000 kowanne.