An tsinci gawar Hakimin Bauchi da aka yi Garkuwa dashi
An kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame a masarautar Bauchi a karamar hukumar Toro a jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi.
Aminiya ta tattaro cewa tun da farko wasu ‘yan bindiga ne da suka kai hari yankinsa suka yi garkuwa da basaraken kauyen a ranar Juma’a, 15 ga Maris, 2024.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ‘yan bindigar sun shiga fadar marigayin kai tsaye daga inda suka yi awon gaba da shi.
An ce marigayin ya yi kwana daya a tsare kafin a kashe shi tare da jefar da gawarsa a kewayen kauyen.
Daga baya kuma wadanda suka shiga aikin neman ceto ne suka dauko gawar.
A ranar Lahadi ne aka kawo gawar tasa a fadar, inda aka yi sallar jana’iza da kuma binne shi.
Daya daga cikin masu rike da mukaman gargajiya na kauyen ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.
Duk kokarin da rundunar ‘yan sandan jihar ta yi domin samun tabbacin hakan ya ci tura, domin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakili, bai dauki wayar ba, ko amsa sakon da aka aike ta wayar salula ta WhatsApp a lokacin da aka buga labarin.