An saki mutumin nan dan Saudiyya da yan sandan Faransa suka kama a Paris bisa zarginsa da hannu a mutuwar dan jaridar nan Jamal Kashoggi.
Mahukuntan Faransa sun bayyana lamarin a matsayin kuskure.
A ranar Talata ne ƴan sanda a Faransa suka ce sun kama wani dan kasar Saudiyya da ake zargi da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi a Faransa.
An kama Khaled Aedh Alotaibi a filin jirgin sama na Charles de Gaulle da ke birnin Paris.
Daga bisani wani jami’in Saudiyya ya ce an yi kamen ne bisa kuskure, kuma tuni aka hukunta wadanda ke da hannu a kisan.
An kashe Khashoggi, fitaccen mai sukar gwamnati a Saudiyya, a karamin ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul a watan Oktoban 2018, inda aka yi gunduwa gunduwa da jikinsa.