An ruwaito cewa an sace Atu Terver, wanda aka fi sani da Krayzeetee, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Benue kan Harkokin Matasa da Yaɗa Labarai.
Rahoton ya bayyana ne a daren Talata bayan matarsa ta wallafa wani saƙo mai cike da kuka da damuwa a shafin sada zumunta.
A cewar ta, ta samu kiran gaggawa daga mijinta cikin tsoro, inda ya ce:
“An sace ni, ki kira mummy.”
Daga baya ba a sake iya samun wayarsa ba.
Terver ya shahara a kwanakin baya bayan ya kori wani daga cikin mataimakansa da ya shiga zanga-zangar adawa da kashe-kashe a Benue.
Hukumomi dai har yanzu ba su tabbatar da labarin sacewar ba, kuma ba a bayyana wani cikakken bayani kan matakan ceto ba.