An sace ɗalibai 15 da kashe mutum hudu a makaranta a Kwalejin Noma Ta Bakura a Zamfara

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Noma da lafiyar dabbobi da ke garin Bakura a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya. 

Mataimakin rijistara na kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar wa da BBC wannan labari.

Ya ce sun kashe mutum huɗu da suka haɗa da ɗan sanda ɗaya da masu gadi uku.

Ya ce “a jiya Lahadi da daddare wajen ƙarfe 10 suka shiga suka yi ta harbe-harbe suka kwashe ɗalibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ƴaƴansa biyu,” a cewarsa.

Malam Aliyu ya ce maharan suna da matuƙar yawa kuma sun haura katanga ne sannan sun fi awa biyu a cikin makarantar suna harbe-harbe.

A watan Yuli ƴan bindiga sun taɓa shiga makarantar ɓangaren gidajen malamai suka sace shugaban Kwalejin ta Bakura. 

Wannan na zuwa bayan ƴan bindiga sun kashe mutum sama da 40 a yankin mulkin Maradun da ke maƙwabtaka da Bakura.

Haka ma ƙaramar hukumar Talatar Mafara da ke maƙwabtaka da Bakura ne ƴan bindiga suka taɓa shiga makarantar sakandaren mata a garin Jangebe suka sace ɗalibai.