An nemi jihohin arewa da su dakatar da hawan babbar Sallah

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga gomnonin jihohin arewaci da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su dakatar da shagulgulan hawan babbar sallah domin dakile bazuwar annobar korona. 

Sakataren gomnatin tarayya kuma shugaban komitin yaki da annobar korona ,Boss Mustapha ya bayyanna haka a cikin wata sanarwa.

Kiran na zuwa ne dai dai lokacin da gomnatin tarayya ta sanya wasu jihohi shida da birnin tarayya na Abuja cikin shirin ko ta kwana kuma ta bas u shawarar amfanin da dokokin dakile yaduwar annobar korona a lokacin shagulgulan Sallah

Jihohin sun hada da Lagos da Oyo da kuma Ribas 

Sauran sun hada da Kano da Flato da kuma Kaduna.

Sai kuma birnin tarayya Abuja.

Haka kuma gomnatin tarayya ta yi kira ga dukannin jihohi da su tsaurara matakan dakile bazuwar annobar korona.

Ya ce gomnatin ta samo ganin karuwa a yawan masu kamuwa da cutar korona kuma wannan abin damuwa ne.