An Kubutar Da ‘Yan Makaranta 21 Da Aka Sace A Arewa Maso Yammacin Najeriya
Akalla dalibai 21 a Najeriya aka kubutar da su sa’o’i bayan da wasu kungiyoyi dauke da makamai suka yi garkuwa da su a yankin arewa maso yammacin kasar da ke fama da rikici in ji ‘yan sanda.
An sace yaran ne a ranar Juma’a a lokacin da suke tafiya tare da malaminsu daga yankin Bakura zuwa makarantar Islamiyya da ke makwabciyarta jihar Katsina, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Mohammed Shehu ya bayyana a karshen mako.
Jami’an tsaro sun mayar da martani tare da kubutar da daliban 21 kuma “a halin yanzu suna aikin ceto sauran wadanda abin ya shafa tare da damke wadanda suka aikata laifin,” in ji Shehu.
Sai dai bai bayyana adadin mutanen da ake garkuwa da su ba, amma ya ce maharan sun kwace matafiya daga motoci kusan biyar, lamarin da ke nuni da cewa akwai wasu da dama har hanzu a hanun yan bindigan.
Sau da yawa ana kai wa kananan yara hari a yankin arewa maso yammacin Najeriya a hare-haren da kungiyoyi masu dauke da makamai ke kai wa a yankunan karkara nesa ba kusa ba daga kariyar jami’an tsaro wadanda galibi ba su da makamai da yawa.
Kwana daya bayan harin da aka kai wa yaran makarantar, rundunar sojojin saman Najeriya ta kaddamar da hare-haren da ta sami nasara ta sama a kan sansanonin ‘yan bindigar da ke jihar Zamfara, kamar yadda babban jami’i Edward Gabkwet ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Litinin. Ya ce ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu a harin jirgin saman ba.
“Za mu bi kowanne daga cikinsu (‘yan bindigar) har sai dukkan ‘yan Najeriya sun sami kwanciyar hankali don gudanar da harkokinsu na yau da kullun,” in ji shi.
A ranar Lahadin da ta gabata, wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe wasu mazauna karkara shida a wasu hare-hare da aka kai a jihar Kaduna da ke makwabtaka da babban birnin Najeriya, a cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar.
Manyan gungun maharan dai galibi sun kunshi samari ne daga kabilar Fulani, wadanda a al’adance ke yin aikin makiyayar shanu, kuma sun shafe shekaru da dama suna rikici da al’ummar Hausawa manoma kan samun ruwa da filin kiwo.