An Kashe Wani Makiyayi, Shanu 50 A Harin Plateau

An Kashe Wani Makiyayi, Shanu 50 A Harin Plateau

Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata sun kashe wani makiyayi da shanu da tumaki 50 a unguwar Fanzo da ke karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.

Alhaji Dan-Azumi, wanda ya yi asarar shanu 21 a lamarin, ya tabbatar wa Aminiya a ranar Larabar da ta gabata cewa wani makiyayi ya samu rauni a lokacin da yake kiwo a yankin.Ya ce, “’yan bindigar sun far wa yankin, suka fara harbe-harbe. Sun kashe daya daga cikin makiyayan tare da jikkata wani.

‘Yan bindigar sun kuma tafi da shanu sama da 50. Wasu daga cikinsu sun mutu, yayin da wasu kuma aka yi musu yankan rago saboda sun riga sun sami raunuka.

Wani hari ne da ba gaira ba dalili.Sai dai ya ce Kwamandan Sector Four ya kira su zuwa wani taro inda ya ce kada su sake kai harin, tare da ba da tabbacin za a binciki lamarin.

Dan-Azumi ya kara da cewa: “Mu ‘yan kasa ne masu bin doka da oda kuma muna kira ga jami’an tsaro a yankin da su yi bincike sosai kan lamarin tare da gurfanar ba da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su kwato mana shanun da aka sace.Shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) na jihar, Garba Abdullahi, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya domin su zama tinkarar wasu.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’, rundunar tsaro da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Samson Zhakom, bai amsa bukatar wakilinmu na neman jin ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.