An Kashe Uba, Da Dansa A Wani Sabon Hari Akan Al’ummar Jihar Filato

An Kashe Uba, Da Dansa A Wani Sabon Hari Akan Al’ummar Jihar Filato

An kashe mutane biyu a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato.

An tattaro cewa harin ya faru ne da daren Asabar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutanen kauyen biyu – uba da dansa.

Daya daga cikin maharan, an bayyana shi ma ya rasa ransa yayin da mutanen kauyen suka fito domin dakile harin.

Wata majiya ta ce mutanen kauyen na tsare da gawarwakin, ciki har da na maharin

Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu hare-hare da aka kai kan al’umomin kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 150 tare da jikkata wasu da dama.

Da yake mayar da martani kan harin na baya-bayan nan, mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’, rundunar tsaro da dama da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Kyaftin James Oya, ya ce lamarin wani lamari ne na yunkurin yin garkuwa da wani Luka Kaze da aka kashe dansa a cikin lamarin.

Oya ya ce a lokacin da sojoji suka fara zuwa aikin ceto, wadanda suka yi garkuwa da su sun harbe daya daga cikin abokan aikinsu cikin kuskure, inda ya kara da cewa dan bindigar ya harbe Kaze ne saboda fushi.