Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Turai ya gano cewa fiye da yara dubu dari uku ne aka kashe a shiyyar arewa maso gabashin kasar, a yakin da ake gwabzawa da `yan boko haram.
Kazalika binciken ya ce fiye da yara dubu biyar na fama da matsaloli daban-daban da suka shafi kwakwalwa, sakamakon rikicin.
Sun fitar da wadannan bayanai da alkaluma ne a cikin wata sanarwa da masu magana da yawunsu a Najeriya, wato Falashade Adebayo da Modestus Chukwulaka suka rattaba mata hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa fiye da yara dubu dari uku ne aka kashe a shiyyar arewa maso gabashin kasar, a yakin da ake gwabzawa da `yan boko haram a cikin shekaru goma sha biyu da suka wuce.
Har wa yau sanarwar ta ce rikicin ya dai-daita ko kuma raba mutum fiye da miliyan daya da gidajensu a shiyyar.
Wata illar da rikicin ya yi wa kananan yara, kamar yadda sanarwar ke cewa ita ce yadda lamarin ya haddasa wa yara fiye da dubu biyar da rikicin ya tilasta musu barin makaranta matsalolin da suka shafi kwakwalwa, kama daga yawan jin takaici da tsarguwa ko firgici da yawan fada ko zafin-rai da sauran matsaloli dangoginsu.