AN KARRAMA MAI BADA UMARNIN SHIRIN KWANA CASA’IN SALISU T BALARABE

A jiya Lahadi Kungiyar Daliban Jihar Kano ta Kasa reshen Jihar Jigawa suka bawa Mai Bada Umarni Salisu T. Balarabe Shaidar Karramawa na Gwarzon Mai Bada Umarni na Fina-finan Hausa masu Dogon Zango, Inda ya samu Shaidar yabon da Shirin nan na Tashar AREWA24 mai dogon zango wato Kwana Casa’in.

A jawabinsa a yayin Taron Salisi T. Balarabe ya nuna farin cikin sa da samun wannan karramawa kuma ya nuna goyon bayan sa ga bawa masu sha’awar shiga shirin daman shiga shirin idan an tashi tantancewa nan gaba musamman dalibai mazauna Jami’ar ta Jigawa wato FUD(Federal University Dutse).
Ya kuma nuna jindadin hadin kai da Jama’ar Jigawan suke bawa Tashar AREWA24 wajen gudanar da shirin Kwana Casa’in, Daraktan ya samu Rakiyar wasu daga Ma’aikatar Tashan AREWA24, daga ciki akwai Evans Ejiogu, Abdulhamid, Muhtadha Abubakar, Lawan Gulu da kuma Ahmad Habib.