An kama mai shirya juyin mulki a Ghana

‘Yan sandan kasar Ghana, sun tabbatar da kama wani fitaccen mai fafutuka da ya jagoranci zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Nana Akufo-Addo bayan ya yi tsokaci a shafukan sada zumunta game da yunkurin juyin mulki.

An kama Oliver Barker-Vormawor shugaban kungiyar masu matsa lamba ta #FixTheCountry wanda ya jagoranci zanga-zanga a kasar  Ghana da ke yammacin Afirka kan matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da kasar ke ciki, a filin jiragen sama a ranar 11 ga watan nan na Febrairun da muke ciki lokacin da ya dawo daga Birtaniya.

Barker-Vormawor ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, zai yi juyin mulki idan majalisar dokokin kasar Ghana ta amince da wani kudiri mai cike da cece-kuce wanda aka fi sani da E-Levy. Kudirin yana gabatar da harajin kaso 1.75 cikin 100 kan hada-hadar kayan lantarki da suka hadar da biyan kudin wayar hannu.

Ana sa ran gurfanar da matashin a gaban kuliya, a ranar Litinin 14 ga wannan wata na Febrairu. Dama dai kasar Ghana ce abin kwatance a yammacin Afirka wajen kwatanta dimukuradiyya mai dorewa, duk da cewa zabukan 2021 na fuskantar zargi daga bangaren ‘yan adawa kan magudin zabe da kuma mutuwar mutane a rikicin zabe.