An kai harin bam a ofishin ‘yan sanda, ofishin INEC a Anambra

Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Laraba sun kashe wani yaro dan shekara 16 a lokacin da suka kai hari ofishin ‘yan sanda da wasu gine-gine da ke cikin ofishin a Nnobi…

Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Laraba sun kashe wani yaro dan shekara 16 a lokacin da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda da wasu gine-ginen da ke cikin ofishin da ke Nnobi a karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

An kuma bayar da rahoton cewa ‘yan bindigar sun raunata wata yarinya ‘yar shekaru 15 da haihuwa.

An kuma ce ‘yan bindigar sun kai harin bam ne a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Ojoto a karamar hukumar.

Yaron da aka kashe dan uwan wani dan sanda ne da ke aiki a ofishin.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai harin bam a hedikwatar hukumar da ke yankin, ta hanyar amfani da bama-bamai (IED).

Majiyar ta ce an kai yarinyar da ta jikkata zuwa asibiti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 1:45 na safiyar Laraba.

A cewarsa, maharan sun zo da yawa a cikin motocin Toyota Sienna guda hudu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce rundunar ta baza jami’an tsaro sosai a fadin jihar domin dakile ci gaba da kai hare-hare a wasu wurare.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a yau 1/2/2023 ta kara karfafa aikin tsaro a jihar, biyo bayan harin da aka kai ofishin hukumar INEC a idemili south, Ojoto da kuma ofishin ‘yan sanda Nnobi.

“’Yan ta’addan sun zo ne da adadinsu da misalin karfe 1:45 na safiyar yau 1/2/2023, dauke da motocin Sienna guda hudu, dauke da bama-bamai, bama-baman mai da sauran ababen fashewa.

“Sun mamaye ofishin INEC da ofishin ‘yan sanda da kuma ginin mazaunin ofishin. Sai dai abin takaicin shi ne, wani yaro dan shekara 16, dan uwan wani dan sanda da ke aiki a ofishin, wasu ‘yan bindiga sun kashe shi, yayin da daya kuma mace ‘yar shekara 15 ta samu rauni a harbin bindiga. An kai ta asibiti inda take jinya.”

A halin da ake ciki, jami’in hulda da jama’a na INEC a jihar Anambra, Dokta Kingsley Agu, bai amsa kiran sa ba, ko kuma ya amsa sakon wayarsa da ya aike ta wayar salula kan harin.