An Kaddamar Da Ayyukan Rajistar Yaran Da Ke Da Tawayar Kwakwalwa A Wasu Jihohin Nijer
A jamhuriyar Nijer wata kungiya mai zaman kanta ta kaddamar da ayyukan rajistar yara masu tawayar kwakwalwa da nufin tantance yawan irin wadanan bayun Allah dake bukatar a basu damar shiga makarantu tun suna kanana ta yadda watan-wata-rana zasu amfani kansu su kuma amfani al’umma.
Rashin wasu alkaluman da ke fayyace takamemen yawan mutane masu tawayar kwakwalwa ne ya sa kungiyar ANPPDI ta shiga yunkurin tattara bayanan da zasu bada damar tantance yawan yaran dake cikin irin wannan yanayi da nufin tunkarar hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa akan bukatar basu kulawar da ta dace musamman a fannin ilimi da kiwon lafiya.
Aiyukan rajistar da za a gudanar a jihohi 3 wadanda suka hada da Damagaram Tilabery da Niamey na hangen kubutar da yaran dake fama da nakasar kwakwalwa daga halin muzgunawar da suke fuskanta daga iyayensu wadanda har yanzu da dama daga cikinsu ke da jahilci akan wannan al’amari.
Shugabanin kungiyar ta ANPPDI sun bayyana fatan samun hadin kan al’umma domin cimma gurin da aka sa gaba a karkashin wannan tsari da ke gudana da tallafin hukumar kare hakkin dan adam ta MDD kamar yadda sakataren kungiyar Alhaji Maman Ado ya bayyana.
Kungiyar ANPPDI wace aka kafa a 1989 na fafitikar ganin jama’a ta maida hankali wajen kula da mutanen da Allah ya jarabce su da matsalar da ta shafi kwakwalwa yaransu da manya.