An harbe wani da ake zargi da satar akwatin zabe a Kogi

An harbe wani da ake zargi da satar akwatin zabe a Kogi

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe wani matashi mai suna Umoru Iduh a mazabar Agala-Ogane da ke babban birnin Anyigba a karamar hukumar Dekina a jihar Kogi ta Gabas saboda yunkurin kwace kayan zabe.

Kamar yadda wani shaidan gani da ido ya bayyana, marigayin ya tunkari sashin kada kuri’a ya dauki BVAS da karfin tsiya ya farfasa a kasa a kokarinsa na halaka su tare da daina kada kuri’a a rumfar zabe.

“Umoru ya fito kwatsam a rumfar zabe da safe, ya dauki BVAS ya fasa a kasa. Bai gamsu ba ya tsaya a kai ya fara tsalle akai-akai, don ya watse.

Wani mutum da ake zargin dan banga ne ya fito daga cikin jama’a ya yi ta harbe-harbe, inda nan take ya kashe shi,” in ji Abdullahi Danjuma wanda ya yi ikirarin cewa yana cikin sashin kada kuri’a a lokacin da lamarin ya faru.

Marigayi Umoru wanda aka ce ya nuna sha’awarsa ta neman shugaban kungiyar masu daukar kaya ta Garage ta Anyigba kwanan nan yana da aure da ‘ya’ya biyu.
An ce dan wani shahararren shugaban matasa ne a garin, Alhassan Agolo.

Sai dai kuma an ce ana ci gaba da kada kuri’a a rumfar zaben duk da kisan da aka yi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya da sauran masu ruwa da tsaki a zaben ba su amsa kira da sakonnin tes ba.