An haramta Memorial International : Rasha

Wata kotu a Rasha ta yanke hukuncin haramta wata kungiyar kare hakkin bil Adama wacce ake kira da sunan Memorial International da wasu sauran rasanta.

Kotun ta ce kungiyar ta karya wasu dokokin kasar na bayyana sunayen wasu fursunonin yan ta’adda da wasu ‘yan siyasar da ake tsare da su a gidajen kurkuku. Kungiyar ta Memorial International wacce wasu ‘yan awaran suka kafa tun a shekara ta 1989 wadanda suka yi adawa da tsohuwar tarrayar Soviet, ta yi ficce a yanzu wajen fafutikar kare hakkin bil Adama a Rasha.