An hana nuna fim kan Nana Faɗima ‘yar Annabi bayan jawo ce-ce-ku-ce

Hukumomin fina-finan Morocco sun haramta fim din nan na Birtaniya mai suna Lady of Heaven da ke janyo ce-ce-ku-ce, bayan da majalisar koli ta addini ta kasar ta yi Allah-wadai da shi.

Fim din ya yi iƙirarin bayar da labarin Nana Fatima, ‘yar Annabi Muhammadu (S.A.W). 

Majalisar ƙoli ta malamai ta ce fim din “karya ce tsagwaronta” kan hujjojin da suka tabbatar da gaskiyar addinin Musulunci.

An yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da fim din a Birtaniya, haka ma Masar da Pakistan da Iran da Iraki sun yi tir da shi.

Majalisar ta zargi fim din da “nuna bangarancin akida “tare da zargin ‘yan fim din da neman suna” kuma sun yi fim din ne domin tayar da husuma tare da “bata ran Musulmi, a cewar kafofin yaɗa labarai na kasar Morocco.

an soki yadda mutumin da ya shirya fim din wanda dan Shi’a ne kuma malamin adinin Musulunci, Yasser Al-Habib, ya bayyana fitattun mutane a farkon zuwan adinin Musulunci wadanda ake girmamawa, inda ya nuna cewa akwai kwatance tsakanin ayyukansu da kuma na kungiyar IS a Iraki.

Mashiryin fim din mai suna Malik Shlibak ya caccaki wadanda ke son a dakatar da fim din a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana shi a matsayin son zuciya, ya kuma ce idan ba sa son fim din kada su kalla a maimakon haramta shi.

Domin sanya talla ko wani labarai da kuke son a saka muku

Haka kuma, a baya ya ce ba dukkan Musulmi ne ke son a dakatar da fim din ba.

Sakamakon zanga-zangar da aka yi a wajen wasu gidajen sinima na Birtaniya, kungiyar masu sinima ta Burtaniya wato Cineworld ta soke nuna fim ɗin na Nana Fatima don “tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatanta da abokan cinikinsu”. 

Wannan kuma ya janyo fushin mutane ciki har da wasu Musulmin da suka so ganin fim din.

Kungiyar masu sinima ta Birtaniya ta dakatar da fim din bayan an yi zanga-zanga a Bolton, da Birmingham da Sheffield.

A Bolton, mutum fiye da 100 ne suka yi zanga-zanga a wajen gidan sinima, in ji Bolton News.

A cikin wani saƙon imel da aka aike wa kungiyar ta Cineworld – wanda kafar yaɗa labarai ta Bolton News ta ruwaito – shugaban majalisar koli ta masallatan Bolton, Asif Patel, ya ce akwai “akidar bangaranci” a cikin fim ɗin kuma “ya yi hannun riga da labaran tarihi da kuma rashin mutunta mutane mafiya daraja a tarihin Musulunci”.