An gano gawar mutum a cikin akwati da aka saya a gwanjo : New Zealand

‘Yan sandan New Zealand na gudanar da bincike bayan wani iyali ya gano gawar mutane a cikin akwatunan da suka saya daga wani gwanjo a wani wurin ajiyar kaya.
Mazauna wani gida a Kudancin Auckland sun gano bakin zaren bayan sun kwashe kayan da aka saya a gidansu.
Hukumomin ‘yan sanda sun kaddamar da binciken kisan gilla tare da kokarin gano gawarwakin.
Ana kyautata zaton dangin ba su da hannu a lamarin.
An fahimci cewa, iyalan sun je dakin ajiyar kaya ne suka sayi tirela mai dauke da kaya – wadanda suka hada da akwatunan – daga wani kamfanin ajiyar kaya a ranar Alhamis din da ta gabata.
An gano lamarin ne bayan mazauna yankin sun dawo da kadarorin zuwa gidansu, in ji sufeto mai binciken Tofilau Faamanuia Vaaelua.
Makwabtan dangin da dama kuma sun ba da rahoton wani “mugun wari” da ke fitowa daga gidan kafin ‘yan sanda su isa, a cewar Stuff.
Wani makwabcinsa – wanda tsohon ma’aikaci ne a wurin konawa – ya ce nan da nan aka gane warin.
“Na sani kai tsaye kuma na yi tunani, daga ina wannan yake fitowa?” In ji shi, yana nufin dukiyar mazauna.
Wata makwabciyarta ta ce danta ya hangi an sauke akwati daga tirelar kafin a sanya shi a cikin wani tanti da aka gina a kusa da harabar.
Hotunan da aka buga a kafar yada labarai ta New Zealand Stuff sun nuna wata motar tirela da aka faka a kan titin gaban gidan, da ke unguwar da ke kusa da wurin shakatawa na Clendon Park, yayin da ‘yan sanda ke gudanar da bincikensu.
Jami’an ‘yan sanda sun ce abin da suka sa a gaba shi ne “tabbatar da gano wadanda suka mutu, ta yadda za mu iya tabbatar da cikakken al’amuran da suka biyo bayan gano lamarin”.
Sun kara da cewa idan aka yi la’akari da “yanayin gano”, zai dauki lokaci kafin a sanar da dangi na gaba.