AN GA RABI’ATU ABDULKAREEM A DAURE A UNGUWAR GAIDA

An ga wata matar aure a daddare a cikin gidanta da musalin karfe 7 na safe a Unguwar Gaida Geza da ke Karamar Hukumar Kumbotso
Mutanen da ke wucewa ta kofar gidan suka ji nimfashi na tashi cikin gidan wanda aka nemi makota suka shiga gidan inda suka iske matar gidan mai suna Rabi Abdulkarim a daudaure tana numfashi sama-sama wanda aka sanar da jami’an yansanda domin bata kulawa gaggawa.