An canja wa coronavirus suna zuwa Covid-19

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce daga yanzu sunan cutar Coronavirus a hukumance shi ne Covid-19.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa, “Yanzu mun sauya wa cutar suna zuwa Covid-19”.

Sauyin sunan ya zo ne bayan karuwar mutuwar wadanda suka kamu da cutar da aka samu wanda ya haura 1000, yayin da wasu dubban mutane kuma suka kamu da ita.

Masu bincike sun bukaci a samar da wani suna ga cutar a hukumance domin a magance rudani da kyamar da ake yi wa masu cutar.

Shugaban hukumar WHO ya ce, “Dole muka samo sunan da ba shi da alaka da sunan wani waje ko wata dabba ko wani mutum ko kuma wata kungiya ta mutane, kuma suna ne da bashi da wuyar fada ba shi kuma da alaka da sunan wata cuta”.

Ya ce “Samun sunan na da matukar muhimmanci domin a kare amfani da sunan da zai iya janyo wata matsala”

An samar da sabon sunan cutar ne daga farkon sunan cutar wato haruffan “Co” daga “corona”, sai “vi” daga”virus” da kuma “d” daga disease”, sannan kuma daga karshe aka sanya shekarar da cutar ta fara bulla wato 2019.

A yanzu haka akwai mutum dubu 42 da dari 200 da aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan China daban-daban.

A ranar Litinin 10 ga watan Fabrairun 2020, mutum 103 suka mutu a rana guda a lardin Hubei, yayin da adadin wadanda suka mutu gaba daya kuma ya kai 1,016.

To amma kuma an samu raguwar masu kamuwa da ita a kasar baki daya inda yanzu ya dawo zuwa kaso 20 cikin 100.

Sakataren lafiya a yankin Hubei, da kuma shugaban yankin, na daga cikin wadanda suka rasa aikinsu saboda zargin sakaci.

A kwanakin baya-bayan nan, mahukuntan China na kara fuskantar suka saboda yadda suke tunkarar annobar.

Mutuwar wani likita wanda tun a farko ya yi gargadi a game da cutar, ya kara janyo suka ga mahukuntan kasar abin da har ya janyo fushin al’ummar kasar ta China.

Yanzu haka dai masana kimiyya daga sassan duniya daban-daban na wani taro a birnin Geneva domin tattauna yadda za a magance yaduwar cutar.

Dokta Ghebreyesus, ya ce har yanzu akwai damar da za a magance wannan cuta idan har aka samu dama da kuma kudi da za a ware domin magance cutar.

Daga nan ya yaba a kan irin matakan da China ta dauka, abin da ya ce ya rage yawan yaduwarta zuwa wasu kasashen duniya.

Amurka ta ce halin da tattalin arzikin China ya shiga zai iya shafar sauran kasashen duniya.