Rahotanni sun bayyana cewa wata mota ta afkawa wani mutum da ke yunkurin kwace waya a lokacin da yake tsallaka titin gidan zoo a jihar Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin sa na sada zumunta a yammacin Lahadi.
Yanzu na samu rahoto daga Zoo Road cewa wani ya dauki wayar wata mata. Yana wucewa sai wata mota ta buge shi. Muna bukatar mu kai shi asibiti.” Inji Kiyawa.
Kiyawa a karin bayani kan lamarin ya ce wanda ake zargin yana samun kulawar likitoci sakamakon raunukan da ya samu.
Ya ce, “Bayan mun kai (mutumin da ya saci wayar) asibiti, sai ya dan yi motsi, kashin bayansa ya karye, kuma kansa ya tsage”, ya kara da cewa asibitin na tunanin kai shi sashen gaggawa.