Amurka za ta fara kwashe jami’anta daga Ukraine
Amurka ta ce barazanar da Rasha ke yi ta soji a Ukraine ta nuna cewa akwai bukatar Amurkan ta kwashe wakilanta da ke ofishin jakadanci a Kyiv babban birnin kasar.
Sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ne ya shaida haka, bayan da shugaban Ukraine din ya nemi a kwantar da hankali, yana cewa babban bakiyin da ke akwai shi ne firgici.
Kasashe da dama sun bai ya mutanensu shawarar su tattara su fice daga kasar.
Moscow da ta girke dakarunta a iyakar Ukraine sama da 100,000 ta musanta cewa tana shirin afkwa kasar Ukraine din ne.
Mai bai wa Fadar gwamnatin Rasha shawara kar harkokin kasashen waje Yuri Ushakov, ya yi watsi da gargadin za a kai hari, yana cewa babu wanda zai musu barazana.
An fara ganin ci gaba a yunkurin kawo sassauci kan rikicin da ke faruwa a yankin a ranar Asabar.
A wata tattaunawar waya da ya yi da Shugaban Rasha a ranar Asabar, Shugaban Amurka ya gargadin Putin kan shirinsu na yin kutse Ukraine.
Ministan tsaron Birtaniya Ben Wallace, ya kwatanta yunkurin diflomasiyya na baya-bayan nan na shawo kan Rasha, a matsayin wani abu da ya yi kama da shawo kan kisan kare dangin da Jamus ta yi a yakin duniya na 2.
Kalaman na sa sun zo ne bayan shugabannin Amurka da na Faransa sun tattauna ta wayar tarho a ranar Asabar da shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Mahukunta da a baya suka yi hasashen cewa lamarin zai kai ga yin gaba da gaba, a yanzu na gargadin cewa akwai alamu masu karfi da ke kara tabbatar da cewa za ta kai ga fadan soji a wannan lokaci.
Fiye da sojojin Rasha dubu ɗari ne ke jiran ko ta kwana a iyakar Ukraine.