Amsar mutane 1,000 wanda suka fi kewar shirin Dadinkowa
Shirin Dadinkowa, wasan kwaikwayo mai dogon zango, mai kuma farin jini da tashar talbijin ta Arewa24 ke gabatarwa ya dade yana jan hankalin masu kallon tashar a ciki da wajen Najeriya.
Shirin da ake nunuwa sau daya sannan a maimaita shi sau biyu a mako, ya kunshi ‘yan wasa daban-daban da ke taka rawa mabanbanta a cikin labaran nishdantarwa shirin.
Yadda zaren labarin shirin ke tafiya da kuma canza salo na yau gareka, gobe ga wanninka, ya sa a kan dade a ba ga mutum ba, wani lokacin ma har sai an manta da shi da kuma labarinsa, sai kuma a wani juyi sai a ga dawo an cigaba da shi.
Mutane a cikin shirin irinsu Sallau kowa na ka, da Badaru, da abokansa Aminu AK, da Rambo, da Wizzy, sun dade suna jan hankalin jama’a a cikin shirin. Haka ma Kabiru Makaho, da Alawiyya, da Nazir, da Gimbiya, da kuma Sa’datu da sauransu.
A shafinta na sada zumunta da muhawara na Facebook, tashar ta yi tambaya na jin ra’ayin jama’a shin wanene suka fi kewar rashin ganinsa? Ni kuma ‘yan kwanaki da yin wannan tambayar, na ziyarci shafin don ganin irin amsoshin da masu bin shafin da kuma ma’abota shirin suka bayar.
Daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Afrilu na shekarar 2021, mutane 982 sun bayyana ra’ayinsu ta hanyar ambaton sunan wanda suke kewarsa a cikin shirin. Ma’ana, wanda a cikin sharin yanzu ba a ganinsa, sakamakon ya mutu a Dadinkowa, ko kuma yana nan, labari ne bai kai kansa ba.
Sunayen da na tattaro a shafin, na mayar da shi wannan hoto ta hanyar fasahar zamani a ke kira Word Art don bayar da labari cikin hikima da jan hankali.
Wannan hoto a taikace shine amsar mutane 982 da suka bayyana ra’ayinsu dangane da wannan tambaya a cikin kalmomi 7,819.
Wannan hoto na Mage idan ka kalla da kyau an samar da shi ne daga rubutu, ma’ana jimlar kalamai 7,819 da aka yi comment a shafin ne. Wadannan na kwaso baki daya na kuma sa a wata manhajar da za ta fito da kalaman da aka fi ambato a rubutun amsoshi. Ma’ana, kowanne digo a cikin wannan hoto, kalma ne na suna, ko na wata jimla da aka rubuta a matsayin amsa.
Girman Kalmar na nuna iya yawan ambatonta da aka yi na wani suna cikin amsohi da bayyana ra’ayi na kimanin mutane 1,000 da su ka yi a shafin. Bisa wannan kididdiga za a iya ganin sunan ‘Gimbiya’ da ‘Aminu’ suna da girma, wanda ke nuna cewa an fi ambaton su ke nan, amma ba su kai girman na ‘Sallau’ ba, wanda ya nuna cewa shi aka fi ambata, don haka sunansa ya fi na kowanne girma a rubutun.
Sauran sunaye da suka fi sauran girma sune na ‘Badaru’ da ‘Malam Ayuba’, da ‘Rambo’ da ‘Aminu AK’ da kuma na ‘Bature’.
Sauran kalmomin da za a iya gani sun fi sauran girma sune ‘malam’, da ‘kewa’, da ‘Allah’ da ‘Ina’ da ‘kowa’. Wadannan sun fito ne saboda irin yanayin da mutane suka bayar da amsar da aka tambayesu ne.
Tashar Arewa24 ta soma shirin wasan kwakwayo na Dadinkowa ne mai dogon zango a shekarar 2014. A wannan zango na farko ta yi kashi sama da dari wanda aka watsa. Cikin wannan shiri ne ‘Badaru da Aminu AK’ suka fito.
A zango na biyu wanda ta yiwa lakabi da ‘Sabon Salo’ tashar ta yi kashi dai-dai har kashi 114, a inda Ayuba Maigadi da Gimbiya da ‘yar uwarta Sa’adatu suka fara fitowa.
A kashi na uku wanda ta yiwa lakabi da ‘Wasa farin Girki’ aka kuma fara shi a tsakiyar watan Yuli, zuwa yanzu ta nuna kashi 78 ana kuma ci gaba da Shirin. A wannan zangon wasan ne ‘Bature’ ya fito. Amma shi Sallau ya fito a duk zangon wasan uku a lokuta daDadinkowa.
Yakubu Liman
Writer|Data Journalist