Amnesty ta zargi hukumomi da ƙoƙarin rufa-rufa kan harin Kaduna
Kungiyar kare haƙƙin dan adam ta Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin ƙasar da ƙoƙarin yin rufa-rufa, wajen ɓoye ɓarnan da aka samu yayin harin da rundunar sojin ƙasar ta kai garin Tudun Biri, da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, da ya janyo asarar rayuka da dama.
A cewar Amnesty International, bincikenta ya gano yadda aka binne sama da mutum 70 a daya daga cikin kaburbura biyu da aka haƙa don binne mutanen.
A hirarsa da BBC, Malam Isah Sanusi, wanda shine daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya ya ce irin wannan hari ya sha faruwa a ƙasar inda ya yi misali da harin da aka kai kan wasu makiyaya a Doma da ke Nassarawa.
Ya ce gwamnati ta yi alƙawarin bincike kan al’amarin amma har yanzu ba a ga komai ba.
Amnesty ta ce ya kamata a yi bincike saboda hakan zai taimaki su kansu sojojin saboda “su kansu sun nuna ba su ji daɗin abin ba.”