Amirka: Matsin lamba ga Biden kan Guantanamo

A Amirka wasu ‘yan majalisun wakilai sun fara matsin lamba ga Shugaban Joe Biden kan ya dauki matakin rufe gidan yarin Guantanamo da ake daure ‘yan ta’adda.

A wata budaddiyar wasikar da suka aikawa sShugaba Joe Biden din dab da zagayowar cika shekaru 20 da kai harin ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumba, ‘yan majalisar wakilan 75 na jam’iyyar Democrats mai mulkin kasar, sun bayyana cewa Amirka na kashe makudan kudi wajen ci gaba da rike ragowar fursinonin da take zargi da kai hare-haren ta’addaci.

Ya zuwa yanzu dai bai wuce fursinoni 39 suke daure a gidan yarin ba, galibinsu tsofaffi ko kuwa wadanda suke da rauni, a cewar ‘yan majalisar. Shi dai gidan yarin Guantanamo da Amirka ta bude a shekarar 2002 da zummar hukunta mayakan Al-Qa’ida da dangoginsu da ta zarga da kitsa kai harin 11 ga watan Satumba, na iya dauar fursuna akalla 800 ne, tare da kashe akalla dala miliyan 500 na kula da su kowace shekara.