Ambaliyar ruwa ta ‘kashe mutum 55, ta lalata gidaje 5,000 a Jamhuriyar Nijar’
Ruwan sama da aka sheƙa kamar da bakin ƙwarya a Jamhuriyar Nijar daga watan Yuni zuwa wannan watan na Agusta ya yi sanadin mummunar ambaliya da ta kashe aƙalla mutum 55 a yankunan jihar Maraɗi da Agadez da kuma babban birnin ƙasar wato Yamai.
Ambaliyar ta kuma lalata gidaje aƙalla 5,000 lamarin da ya tilasta wa kusan mutun 53,000 gudun hijira, kamar yadda rahotanni suka nuna.
A ƙaramar hukumar Ɗan-Isa da ke gundumar Mada-rumfa da ke jihar Maraɗi, an samu ambaliyar da ta sa al’ummar da suka rasa matsugunansu fakewa a gidajen ƴan uwa da abokan arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Ɗan-Isa Alhaji Adamu Gerau ya tabbatar wa da BBC cewa ”mun ƙirga kusan gidaje fiye da 150 da suka lalace bayan ambaliya. An kuma rasa gonaki da dama.”
”Bayan haka an samu asarar rayuka don mutun hudu sun rasu sanadin ambaliyar,” in ji shi.
A cewar shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Maradi, Malam Abbas Haruna ɗan Adu’a, a jihar tasu kawai lamarin ya shafi magidanci 4,948 da hukumomi suka tantance don taimaka musu.
Amma ya ce akwai buƙatar masu hannu da shuni su shigo cikin lamarin, don su taimakawa gwamnati ganin cewa takalihu ne da ba za iya ba ita kaɗai.
Ya ƙara da cewa yanzu haka suna da ton 150 na kayan abinci da za a raba wa waɗanda ambaliyar ta shafa.
Dama hukumar da ke lura da hasashen yanayi a Jamhuriyar Nijar ta yi hasashen faduwar ruwan sama mai yawa a bana.
Ko a bara mutum 73 suka mutu sanadiyyar ambaliya a Nijar, yayin da wasu miliyan biyu suka shiga mawuyacin hali a cewar rahoton majalisar ɗinkin duniya.