Ambaliyar ruwa a Sudan ta kashe mutane 77 tare da lalata gidaje 14,500

Ambaliyar ruwa a Sudan ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata gidaje kimanin 14,500 a daidai lokacin da ruwan sama ya mamaye kasar, lamarin da ya janyo ambaliyar ruwa da lalata dukiyoyi.
Adadin wadanda suka mutu tun lokacin damina ta fara a watan Mayu ya kai 77, in ji kakakin majalisar tsaron farar hula ta Sudan, Birgediya Janar Abdul-Jalil Abdul-Rahim, a ranar Alhamis.
Lardunan da ruwan sama ya fi shafa sun hada da North Kordofan, Gezira, South Kordofan, South Darfur da kuma kogin Nile, in ji kakakin.
Ana yawan samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a Sudan a tsakanin watan Mayu zuwa Oktoba, kuma kasar na fuskantar ambaliyar ruwa a duk shekara da ta lalata dukiya, kayayyakin more rayuwa da kuma amfanin gona.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya bayar da rahoto a farkon wannan makon cewa, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta gwamnati, da kungiyoyin jin kai, da kuma hukumomi, fiye da mutane 136,000 ne ambaliyar ta shafa.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana sa ran adadin wadanda ambaliyar ta shafa zai karu yayin da ake ci gaba da gudanar da tantancewar kuma an yi hasashen samun ruwan sama mai karfin gaske. Majalisar Dinkin Duniya ta kuma ce adadin mutane da yankunan da ruwan sama ya shafa a ranar 14 ga watan Agusta ya “ ninka” idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Kimanin mutane 314,500 ne lamarin ya shafa a duk fadin kasar Sudan a duk lokacin damina a shekarar 2021, a cewar MDD.
A shekarar 2020, hukumomi sun ayyana Sudan a matsayin wani yanki na bala’i tare da kafa dokar ta baci na tsawon watanni uku a duk fadin kasar bayan da ambaliyar ruwan ta kashe mutane kusan 100 tare da mamaye gidaje sama da 100,000.