Ambaliya: Zulum ya fita karfe 6 na safe don duba inda ruwa ya yi wa aiki
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fita da sassafe wurin karfe 6 na ranar Juma’a don duba wuraren da ambaliyar ruwa ya shafa a cikin birnin Maiduguri.
Fitar gwamnan ya yi ta ne don dubawa tare da kawo mafita game da babbar matsalar ambaliyar ruwa da ta dade tana ci wa jihar tuwo a kwarya.
Yankunan da Gwamnan ya ziyarta sun hada da Dala Dolori Tudu, Jiddari Polo, Galadima, tsohuwar Maiduguri da yankin Bulumkutu.
A tawagar Zulum, akwai kwamishinan muhalli, dan majalisa mai wakiltar mazabar Jere ta tarayya da kuma sauran mambobin kwamitin jihar na yaki da ambaliyar ruwa a Maiduguri da Jere.
A yayin ziyarar, Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci ma’aikatar muhalli da ta tabbatar da cewa ta kammala duba wurin da gaggawa, wanda hakan zai sa a shawo kan matsalar da gaggawa.
Idan za mu tuna, a ranar 6 ga watan Satumban 2019, Gwamna Zulum ya bada umarnin fara bincike tare da hadin guiwar cibiyar kula da annoba ta jami’ar Maiduguri.
A matsayin hanyar taimakon gaggawa, Gwamna Zulum ya bada umarnin cike tafkunan ruwa da ke yankin Bulumkutu da Dala.
Baya ga duba ambaliyar ruwan, Zulum ya duba yadda ake ginin sabuwar babbar makarantar sakandare da ke tsohuwar Maiduguri, da titi mai nisan kilomita 10 tare da magudanun ruwa da ke Jiddari Polo.
A wani labari na daban, Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya ce idan rundunar sojin Najeriya ba za su iya tsare Baga ba, zai sa mafarauta su tsare masa garin.
A ranar Laraba, mayakan ta’addancin Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan farmaki a yayin da take kan hanyar ziyartar sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.
Bayan bada motocin sintiri 12 ga jami’an tsaro a yankin, Zulum ya kaddamar da sake bude babbar hanyar Monguno zuwa Baga bayan rufeta da aka yi na shekaru biyu.
Zulum, wanda tun farko ya yi jawabi ga rundunar sojin a kan cewa babu ‘yan ta’addan a Baga, ya koma inda ya tambayesu yadda aka hari tawagarsa.