Agenda Na Kadai Shine Na Yiwa ‘Yan Nijeriya Hidima – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya ce ba shi da wata manufa Illa ya Ceto ‘Yan Nigeria.
Ya bayyana haka ne a garin Yola na jihar Adamawa a jiya a wani taron da dubban magoya bayan jam’iyyar APC na jihar suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Atiku wanda gungun jama’a suka tarbe shi a dandalin Mahmud Ribadu da ke Yola, ya ce zai magance kalubalen da Najeriya ke fuskanta idan aka zabe shi.
Wannan dai shi ne karon farko da ya koma garinsu bayan ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.
Atiku ya bukaci al’ummar jihar Adamawa da su hada kai da goyon bayan da suke ba shi tsawon shekaru 30 da ya shafe yana siyasa.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su hada kai su yi aiki tare.
A halin da ake ciki, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya ce ba zai sauka daga mulki ba duk da matsin lamba da aka yi masa na yin hakan.
An ce, Ayu na fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mukaminsa a wani bangare na sharuddan sasanta rikicin da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Tun bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar da kuma tsayar da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa Atiku da Wike dai na takun saka tsakanin Atiku da Wike.
Sai dai Ayu ya ce bai yi murabus ba, kuma ba shi da wani shirin yin hakan, yana mai cewa a shirye yake ya jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasara a 2023.
“Saboda haka, mun sake bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, bai yi murabus ba, kuma ba shi da shirin yin murabus. Domin a fayyace da kuma ba da muhimmanci, an zabe shi na tsawon shekaru hudu,” in ji mai taimaka wa Ayu kan harkokin yada labarai, Simon Imobo-Tswam, a cikin wata sanarwa jiya.
Kakakin jam’iyyar PDP, Honarabul Debo Ologunagba, ya musanta cewa bai san wani sharadi daga sansanin Wike da ke neman shugaban jam’iyyar na kasa ya sauka daga mulki ba.