Abubuwan da manyan ‘yan siyasar suka tattauna : Tinubu da Shekarau

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau sun gana a karon farko tun bayan rikici ya barke a jam’iyyar tasu reshen jihar Kano.

Rikicin , wanda ya sa Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano ballewa daga bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka kira kansu G-7, ya kuma sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na jiha.

A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wadannan zabuka sun raba kawunan ‘yan jam’iyyar ta APC a a jiar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya. Hasalima rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau suna yi wa juna shagube.

Sanata Shekarau ya shaida wa Jaridar BBC Hausa cewa rashin iya jagorancin jam’iyya daga Gwamna Ganduje ne

Sai dai hukuncin da wata babbar kotu a Abuja ta yi a makon jiya ya ayyana bangaren Sanata Shekarau a matsayin halastaccen bangare a zaben shugabannin jam’iyyar.

Amma wannan hukunci bai yi wa bangaren Gwamna Ganduje dadi ba inda ya sha alwashin kalubalantarsa a kotu ta gaba.

‘Dinke baraka’

An yi ganawa tsakanin Shekarau da Tinubu ne ranar Lahadi a gidan tsohon gwamnan jihar ta Lagos da ke unguwar masu hannu da shuni da ke Ikoyi.

Wani makusancin Shekarau, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya gaya wa BBC Hausa jiga-jigan jam’iyyar ta APC sunb tattauna ne a kan rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar reshen jihar Kano.

Ya kara da cewa Tinubu da kansa ne ya bayar da jirgi aka je Abuja aka dauki Shekarau domin ya sulhunta shi da Gwamna Ganduje.

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun yunkurin sasanta bangaren Ganduje da na Shekarau amma hakan ya ci tura.

Kazalika rikicin ya kara kamari sakamakon zargin da Sanata Barau Jibrin da ke wakiltar Kano ta Arewa, kuma daya daga cikin jiga-jigan APC da ke bangaren Shekarau, ya yi cewa bangaren Ganduje ne ya kona masa ofishin siyasarsa a makon jiya.

Sai dai bangaren na Ganduje ya musanta zargin.

Masana harkokin siyasa na cewa yunkurin da Tinubu yake yi na sulhunta Ganduje da Shekarau ba ya rasa nasaba da bukatar kashin kasa musamman sabda rade-radin da ake yi cewa yana son tsayawa takarar shugaban Najeriya a 2023. Kuma kasancewar Kano a matsayin jihar da ke da miliyoyin masu kada kuri’a ba zai so jam’iyyar APC ta rasa ta ba.