Babu wanda zai sha gabanmu wajen samar da ingantaccen fetur — Dangote
Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa sabuwar matatar da ke Legas za ta soma fitar da man fetur mai inganci a farashi mai rahusa haka kuma babu wanda zai sha gabansu wajen samar da ingantaccen fetur.
Bayan ta shafe sama da shekara guda tana aiki, matatar ta Dangoten a halin yanzu ta soma samar da fetur.
Matatar wadda a baya take iya tace gangar mai 350,000 a duk rana, a halin yanzu ana sa ran za ta iya tace iya ƙarfinta da aka sanar na ganga 650,000 a kullum zuwa ƙarshen shekara.
Hakan zai zama wani babban ci gaba ga ɓangaren makamashi na Nijeriya. Dangoten ya ƙara shaida wa manema labarai cewa “wannan ranar murna ce ga ‘yan Nijeriya.”
“Da zarar mun kammala warwarewa da NNPCL, kayayyakinmu za su soma shiga kasuwa. Za mu taimaka wurin farfaɗo da masana’antu.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu ƙarin kuɗin mai a Nijeriya, lamarin da ya ƙara saka ‘yan ƙasar da dama ƙorafi.
A ranar Talata ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin.
Bayanai daga sassan Nijeriya daban-daban na cewa sabon farashin ya bambanta, inda ake sayar da lita daya a Legas a kan naira 855 yayin da a wani bangare na shiyyar arewa maso yamma kuma ake sayar da shi a kan naira 904.