‘Yan Sanda Sun Kama Jami’in Sojin Ruwan Da Ya Kashe Aminu

‘Yan Sanda Sun Kama Jami’in Sojin Ruwan Da Ya Kashe Aminu

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama wani jami’in sojan ruwan Najeriya, Abdul Rasheed Muhammad da laifin kashe Aminu, dan tsohon babban hafsan sojin ruwa Vice Admiral I. I. Ibrahim (mai ritaya).

Kwamishinan ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, Bennett Igweh, yayin da yake gabatar da wanda ake zargin ya ce Muhammad ya kashe Aminu ya kuma sace motar sa makonni biyu da suka gabata.

Ya ce, “Kusan makonni biyu da suka gabata, an yi wa Aminu Ibrahim, dan Vice Admiral I. I. Ibrahim (mai ritaya), tsohon babban hafsan sojin ruwa, fashi da makami a unguwar Maitama da ke Abuja, sannan aka dauki motarsa ​​kirar Prado SUV.

“Ina so in sanar da ku cewa, Abdul Rasheed Muhammad, wani jami’in sojan ruwa na Najeriya ne ya aikata kisan. Ya amsa laifinsa, kuma mun kwato motar Prado Jeep.”

Da yake magana da ‘yan jarida, Muhammad ya ce shi ma’aikacin jirgin ruwa ne a cikin sojojin ruwa da aka tura gidan tsohon babban hafsan sojin ruwa.

Ya ce, “Ina aiki a gida. Ya so fita da daddare, wajen 11:30. Yace yana bukatar tsaro.

“Don haka, na bi shi da bindiga ta. A hanya ya tsaya ya duba ATM dinsa, kamar zai sayi wani abu.

“Na yi tunanin watakila zan raka shi kasuwa ko wani wuri. Sa’an nan, da na fito ta daya kofa, na harbe shi, na dauki mota, na tafi. Ni mai gadi ne kuma ma’aikacin jirgin ruwa a cikin sojojin ruwa. Bai yi mini kome ba; Na kashe shi ne don satar motarsa.”