Ƴan sanda sun cafke matashin da cinna wa masallaci wuta a Kano

Ƴan sanda sun cafke matashin da cinna wa masallaci wuta a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wani matashi da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta a lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.

Al’amarin dai ya faru ne a a ƙauyen Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa.

A wata sanarwar da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai suna Shafi’u Abubakar mai shekara 38 ya yi sanadiyyar ƙonewar mutane.

Tuni dai aka kwashe mutum 24 waɗanda suka ƙone zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu, kuma mutum ɗaya ya rasu.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa binciken da aka gudanar dai ya nuna cewa an yi amfani da man fetir ne wajen cinna wutar.

Dangane kuma da dalilin faruwar al’amarin, SP Kiyawa ya ce “matashin ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙin raba gado a tsakanin danganinsa, inda ya ce waɗanda suka zalunce shi ɗin suna cikin masallacin a lokacin da suke sallah. Kuma ya yi hakan ne domin ya aike da saƙo.” In ji matashin.