Yan Najeriya 2,583 aka kashe , an sace 2,164 a cikin watanni 3

Yan Najeriya 2,583 aka kashe , an sace 2,164 a cikin watanni 3

Akalla mutane 2,583 ne aka kashe tare da yin garkuwa da 2,164 a rubu’in farkon wannan shekarar, kamar yadda wani bayanai daga Beacon Security and Intelligence Limited, wani kamfani mai kula da hatsarin tsaro da leken asiri da ke Abuja ya nuna.

Alkalumman da suka nuna adadin kashe-kashe da sace-sacen jama’a a fadin kasar daga watan Janairu zuwa Maris, sun nuna cewa kashi 80 cikin 100 na kashe-kashen da kuma kashi 94 cikin 100 na sace-sacen sun faru ne a Arewa.

Sai dai wannan rahoto ya ci karo da matsayin da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya amince da shi, inda ya ce alkaluman wadanda suka mutu na raguwa.

Rahoton kamfanin tuntubar ya nuna cewa an kashe mutane 28 tare da yin garkuwa da mutane 24 a kullum.

Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan a farkon wannan wata a yayin taron lacca na shekara-shekara da cibiyar samar da ayyukan yi ta sojojin Najeriya ta shirya a Abuja, ya ce an samu saukin matsalar tsaro.